1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta kai harin rokoki a Zirin Gaza

April 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bv2h
Akalla mutane 6 suka riga mu gidan gaskiya a wani hari da jiragen saman yakin Isra´ila suka kai akan wani filin atisaye na wata kungiyar Falasdinawa ´yan gwagwarmaya dake Zirin gaza. Hukumomin yankin sun ce wani jirgin saman yakin Isra´ila ya harba rokoki guda uku, daya ya fada akan wata mota yayin biyu suka fada akan wani gini. Daga cikin wadanda suka rasu a harin har da shugaban wata kungiyar ´yan takife da kuma wani karamin yaro. A wani labarin kuma sabuwar gwamnatin Hamas ta kulla yarjejeniyar ba juna cikakken hadin kai da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas a wani yunkuri na tinkarar barazanar matsalolin kudi da hukumar mulkin Falasdinu zata fuskanta. Bayan tattaunawa ta tsawon sa´o´i 4 da shugaba Mhamud Abbas an jiyo FM Isma´il Haniya na cewa duk da banbancin ra´ayi dake tsakanin su, sassan biyu zasu ba juna hadin kai. Da farko dai Amirka da kuma KTT sun katse bawa hukumar mulkin Falasdinu taimako kai tsaye.