Isra´ila ta kai hari a Zirin Gaza bayan harin kunar bakin wake da aka kai mata | Labarai | DW | 30.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta kai hari a Zirin Gaza bayan harin kunar bakin wake da aka kai mata

Jiragen saman yakin Isra´ila sun yi ruwan bama-bamai akan wata hanyar karkashin kasa dake Zirin Gaza, wadda aka yi zargin cewa sojojin sa kai na Falasdinawa na amfani da ita wajen kai hare hare kan Isra´ila. Wannan shi ne karon farko da aka kaiwa Gaza farmaki ta sama tun bayan da Isra´ila da kungiyoyin gwagwarmaya na Falasdinawa suka kulla wata yarjejeniyar dakatar da yaki cikin watan nuwamban bara. Harin ya zo ne kwana guda bayan wani harin kunar bakin wake da ya halaka mutane 3 a wani gidan gasa burodi dake birnin Eilat na Isra´ila. Harin kunar bakin wake shi ne na farko da aka kaiwa Isra´ila a cikin watanni 9 kuma na farko da aka kai a birnin dake kudancin Isra´ila. Kungiyoyin Falasdinawa guda 3 sun yi ikirarin kai harin.