Isra´ila ta kai hare hare guda 250 cikin sa´o´i 7 a kudancin Libanon | Labarai | DW | 05.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta kai hare hare guda 250 cikin sa´o´i 7 a kudancin Libanon

Karon farko a fadan da aka shafe sama da makonni 3 ana yi, wata rundunar sojin Isra´ila ta tsokani sojojin Libanon dake birnin Tyre mai tashar jiragen ruwa. Sojojin sun bude wuta bayan da alikoptocin yakin Isra´ila suka harba rokoki da dama kana kuma suka sauke mayakansu na kasa a yankin. An halaka akalla mutane 5 yayin da da dama suka jikata. Isra´ila ta ce sojojin ta 8 sun samu rauni yayin da Hisbollah ta yi ikirarin fatattakar sojojin. Kamar yadda hukumomin Libanon suka nunar jiragen saman yakin Isra´ila sun kai hare hare mafi muni a kudancin kasar tun bayan da Isra´ila ta fara yiwa yankin lugudan wuta a ranar 12 ga watan yuli. Rahotanni suka ce a cikin sa´o´i 7 an kai hare hare ta sama har 250, inda daya bayan daya aka lalata kauyuka 15 dake kusa da kan iyakar kasashen biyu. Su ma mayakan Hisbollah sun harba rokoki cikin Isra´ila ciki har da unguwannin dake wajen birnin Haifa, inda suka raunata mutum 5.