Israila ta jibge dakarun ta zirin Gaza | Labarai | DW | 27.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila ta jibge dakarun ta zirin Gaza

Israila ta jibge sojoji da tankunan yaki a kan iyakar zirin Gaza a matakin shirin kai mummunan farmaki yankin na Gaza bayan sace wani sojin Israila da yan takifen Palasdinawa suka yi a ranar lahadin data gabata. Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas ya ya umarci jamián tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano inda aka yi garkuwa da sojin don kaucewa farmakin na Israila. A halin da ake ciki wasu kungiyoyi uku na Palasdinawa wadanda suka hada da reshen Hamas mai tsatsauran raáyi sun bukaci a sako dukkanin matan Palasdinawa da kananan yara da Israila ke tsare da su a gidajen yari kana su kuma su bayar da bayanin inda sojan da aka yi garkuwa da shi din yake. Israilan dai ta yi wasti da wannan bukatar. A waje guda kuma sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya yi kiran yin taka tsantsan da nuna sanin ya kamata, a yayin da Israila take jibge sojojin ta da shirin kai farmaki a kan yankin Gaza. Annan ya bukaci bangarorin biyu su nuna dattako tare da bin matakan da suka dace domin kawar da tashin hankali da zubar da jini.