Isra´ila ta gargadi Iran game da shirin ta na nukiliya | Labarai | DW | 22.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta gargadi Iran game da shirin ta na nukiliya

Ministan tsaron Isra´ila Shaul Mofaz ya ce kasarsa ba zata taba amincewa Iran ta mallaki makaman nukiliya ba. Ko da yake a wani jawabi da yayiwa babban taron jami´o´i a kusa da birnin Tel Aviv mista Mofaz bai ce ko Isra´ila na shirin daukar matakan soji kan Iran ba, amma ya ce kasar Bani Yahudu ba zata tsaya haka kawai ta ga Iran ta mallaki makaman nukiliya ba. Mofaz, wanda haifaffen kasar Iran ne, ya yi kakkausar suka ga shugaba Mahmud Ahmedi Nijad, inda ya ce idan shugaban bai daina kiran da a gusar da Isra´ila ba, to shugaban zai janyowa al´umarsa wani mummunan bala´i ne. Iran dai ta ce shirin ta na nukiliya na samar da wutar lantarki ne amma ba na tashin hankali ba, to amma kasashen yamma musamman Amirka na zargin ta da shirin kera makaman nukiliya a boye.