Isra´ila ta fara janyewa daga Zirin Gaza | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta fara janyewa daga Zirin Gaza

Rundunar sojin Isra´ila ta fara janyewa daga arewacin Zirin Gaza bayan wani kutse na mako daya wanda yayi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 52 da sojin Isra´ila daya. Isra´ila ta ce ta dauki matakin sojin ne don hana sojojin sa kan Falasdinawa harba rokoki zuwa wani yankin Isra´ila dake kusa. To amma kafofin yada labarun Bani Yahudu sun rawaito cewar sa´o´i kalilan bayan an fara janyewar, dakarun Isra´ila sun kashe Falasdinawa 5 ciki har da masu gwagwarmaya biyu a rewacin Gaza. A kuma halin da ake ciki shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da FM Ismail Haniyeh sun tattauna da nufin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa amma kawo yanzu sun kasa dinke barakar dake tsakaninsu.