1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta datse ruwan sha ga yankin Gaza

October 9, 2023

Ministan lantarki na Isra'ilan shi ne ya bayar da wannan umarnin na gaggawa, a wani martani dangane da hare-haren da Hamas ta kai wa Isra'ilar.

https://p.dw.com/p/4XJKk
Gaza City | Trinkwasser aus der Luft | Unternehmen Watergen
Hoto: Adel Hana/AP Photo/picture alliance

Hukumomin Isra'ila sun bayar da umarnin datse hanyar bayar da ruwan sha ga yankin Gaza nan take, a daidai lokacin da suke ci gaba da luguden wuta ta sama kan yankin na Falasdinawa. Ministan lantarki ne ya bayar da wannan umarnin na gaggawa, jim kadan bayan da ministan tsaro Yoav Gallant ya bayar da umarnin yi wa Gaza kawanya.Kashi 10 cikin 100 na ruwan sha da ke zuwa Gaza, yana fitowa ne daga Isra'ila.