1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta cire na'urorin bincike a masallacin Al-Aqsa

Gazali Abdou Tasawa
July 25, 2017

Gwamnatin Isra'ila ta janye na'urorin binciken da ta girka a kofofin masallacin Al-Aqsa, matakin da ya haifar da tarzoma a birnin Kudus da ma a wasu kasashen Larabawa a baya bayan nan. 

https://p.dw.com/p/2h5W7
Israel - Palästina - Konflikt - Unruhen
Hoto: Reuters/K. Abdullah

Gwamnatin Isra'ila ta janye na'urorin binciken da ta girka a kofofin masallacin Al-Aqsa, matakin da ya haifar da tarzoma a birnin Kudus da ma a wasu kasashen Larabawa a baya bayan nan. 

Fadar firaministan kasar ta isra'ila ce ta sanar da janye na'urorin binciken a sakamakon matsin lambar da ta fuskanta daga kasasahen duniya da dama wadanda suka bayyana fargabar ganin rikicin ya yadu zuwa sauran kasashen Musulmin duniya da na larabawa. Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa wani dan jaridarsa ya gane wa idanunsa lokacin da ake aikin cire na'urorin binciken tun da sanhin safiyar wannan Talata. 

Kasashen duniyar dai sun bai wa mahukuntan tsaron kasar ta isra'ila da maye gurbin na'urorin binciken da wasu fasahohin bincike na zamani da ba sa jan hankalin jama'a ba tare da yin bayani kan nau'irin fasahohin binciken da suka dace ba. Sai dai wasu shaidun gani da ido sun ce an kafa kyamarorin a wasu kofofin shiga masallacin wanda ke zama na uku wajen daraja a idon Muslmin duniya.