1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Isra´ila ta cika shekaru 60 da girkuwa

A kwana a tashi an cika shekaru 60 da girka ƙasar Isra´ila.

default

Shekaru 60 da girka Isra´ila


A wannan karo shirin zai kai mu Isra´ila, inda za muyi waiwaye adon tafiya, albarkacin cikwan shekarau 60 daidai da kafa wannan ƙasa.

Za mu ga yadda aka girka ta, da kuma matsalolin da suka biyo baya, tsakanin bani yahudu da larabarawa, wanda har yanzu ke cigaba da tada hasumi  a yankin gabas ta tsakiya, da ma fagen siyasa duniyar baki ɗaya.


A kwana a tashi, ƙasar Isra´ila ta cika  shekarau 60 daidai da girkuwa.

A matsayin waiwaiye adon tafiya mu tunatar da ku cewar,

 a shekara za 1897 ne wani bayahude mai suna Theodore Herzl, ya shirya gagaramin taro, wanda ya haɗa tawagogin yahudawa daga sassa dabam dabam na duniya, da zumar tunani, a game da hanyoyin girka ´yantaciyar ƙasar da za ta tattara yahudawa dake warwatse ko ina cikin duniya.

Bayan yaƙin duniya na biyu ,Majalisar Ɗinkin Duniya ta wacen lokaci, ta miƙawa ƙasar Britaniya renan Falestinu.

A lokacin, ƙasar na da jama´a dubu ɗari 7,  larabawa fiye da dubu ɗari shida, sai kuma bani yahudu ƙasa da dubu ɗari.

Yahudawa bisa jagorancin Dr Haim Weizmann, sun ci gaba da faɗi ka tashi, domin cimma burin Theodore Herlz.

A game da haka,suka yi roko ga gwamnatin Britaniya, ta dubi wannan buƙata da idon rahama, mussamman a daidai lokacin da yahudawa ke fuskantar uƙuba da azaba, inda dubunnai suka rasa rayuka a Turai.

Ranar 2 ga watan november ministan harakokin wajen Britaniya James Balfour, ya karanta wata sanarwar da aka fi sani da suna sanarwar Balfour, wace a cikinta Britaniya ta yi na´am da girkawa yahudawa ƙasa.

Saidai ra´ayoyin sun rarrabu gida uku a game da yankin da za  a gina wannan ƙasa.

An ambata sunayen ƙasashen Argentina da Uganda a nahiyar Afirka, kamin daga bisani a cimma daidaito ga kasar Palestinu.

Bayyana sanarwar ke da wuya yahudawa suka ci gabada yin turuwa zuwa Palestinu.

Ƙasashen larabawa, mussamman na yanki gabas ta tsakiya, sun bayyana  mummunar adawa ga sarnawar Balfour da kuma kwarara bani yahudu a Palestinu.

A game da haka, tashe tashen hankulla suka ɓarke tsakanin shekara ta 1920 zuwa 1921 a biranen Qudus, Hebron, Jaffa da Haifa.

yahudawa da dama suka rasa rayuka  a cikin wannan arangama.

A dalili da wannan yanayi, fadar mulki a birnin London, ta yanke hukunci dasa aya ga kwarara bani yahudu zuwa Palestinu, matakin da baiwa ƙungiyoyin fafatakar ƙwatar ´yancin yahudawa daɗi ba.

A shekara ta 1945 bayan yaƙin duniya na biyu ,jam´iyar Labor ta karɓi ragamar mulkin Britaniya.

A yaƙin neman zaɓe jam´iyar  ta alƙawarta ɗage dokar hana yahudawa shiga Palestinu, tare da jaddada aniyar girka masu ƙasa  a cikin Palestinu.

Wannan mataki ya ci karo da turjiya daga ƙasashen larabawa, abinda ya cilastawa gwamnatin Britaniya lashe amenta.

To saidai bisa matsin lambar Amurika da wasu ƙasashe masu faɗa aji, Britaniya ta baiwa yahudawa dubu 100 damar shiga Palestinu.

A dangane da martanin ƙasashen larabawa, Britaniya ta yada  ƙashi domin ta huta da ƙuda, wato ta maidawa Majalisar Ɗinkin Duniya renan Palestinu da aka danƙa mata.

Majalisar ta girka wani komiti na mussamman, wanda yayi nazari a dangane da rabon ƙasar Palestinu.

Ranar 29 ga watan November na shekara ta 1947, taron Majalisar Ɗinkin Duniya, ya amince da fasalin komitin, wanda ya tanadi karkasa Palestinu a gida ukku: kashi ɗaya ga Palestinawa, ɗaya ga yahudawa, sannan birnin Qudus da kewaye ya kasance cikin kullar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Shugaban ƙasar Amurika Henry Thruman ,da Russia suka yi ruwa da tsaki, domin cimma wannan mataki.

Ba da wata wata ba, ƙasashen larabawa suka yi watsi da abunda suka ka danganta da haramtacen rabo, a yayin da yahudawa suka yi lale marhabin da shi.

Wannan watanda da  Majalisar Ɗinkin Duniya tayi da ƙasar Palestinu ya haifar da rikici mai muni tsakanin ɓangarorin biyu.

Dakarun Palestinawa na samun tallafi daga ƙasashen larabawa a yayin da Isra´ila ke samun goyan bayan daga Amurika.

A cikin wannan yanayi ne, ranar 14 ga watan mayu na shekara ta 1948, Isra´ila ta bayyana kanta a matsayin ƙasa mai cikkaken ´yanci.

Itakuwa Britaniya ta fice daga Palestinu.

Ƙasashen Masar da Syria, sun aika dakarunsu domin kora sojojin Isra´ila daga yankunan Palestinawa da suka mamaye.

Dakarun biyu sun tafka faɗa kamin a cimma yarjejeniyoyin tsagaita wuta, wanda ba su tsinana komai ba, ta fanni samar da zaman lahia.

Daga shekara ta 1964, shugabanin ƙasashen larabawa suka amince da bada haɗin kai ga ƙungiyar PLO ta Yassser Arafat, wada suka ɗorawa yaunin  ƙwatar yancin Palestinu tare da bata tallafin da ya dace.

Saidai duk da haka, Isra´ila ta ci gabada bunƙasa makamai wanda suka kaita ga matsayin gagarabadau ta fannin yaƙi, a sakamakon haka ta faɗaɗa matsugunanta a Palestinu, tare da mamaye wasu ƙarin yankuna mallakar Masar da Syria kamar su tudan Golan da Sinai.

Ƙasashen sun ƙaddamar da yaƙi a watan okober na shekara ta 1973 da aka fi sani da yaƙin Kippour, kimanin sojoji dubu huɗu suka rasa rayuka daga ɓangarorin biyu.

Shugaban ƙasar Amurika Jimmy Carter ya gayyaci Isra´ila da Palestinu zuwa tebrin shawara a Camp David, wanda a sakamakon hakan, aka cimma yarjeniyar farko ta tasagaita wuta ranar 26 ga watan Maris na shekara ta 1979.

Jim kaɗan bayan kaiwa ga wannan mataki Jimmy Cater yayi bayyani da cewar:

Tsawan shekaru ukku ana gwabza faɗa, tsakanin Isra´ila da Masar, a tsukin watanni shiga, sun shiga tattanawa, wacce ta kai ga cimma matakin zama lahiya.


Shugaban ƙasar Masar na zamanin Annouar El Sadate da ya rattaba hannu a kan yarjeniyar ya hurucu kamar haka:


Wannan lokaci ne na tarihi, ga dukkan ma´abuta zaman lahia.


Bayan rattaba hannu akan wannan yarjeniya an samu lafawar

ƙura tsakanin Masar da Israela, to saidai ba a cimma abun azo a gani ba, a game da tushen rikicin na tsakanin.

An ci gabada tattanawa ta ƙasa da ƙasa, wada a sakamakon ta ɓangarorin biyu suka cimma yarjeniyar Oslo a shekara ta 1993, inda gwamnatin Israela ta amince da ƙungiyar PLO a matsayin abikiyar tattanawa.

Fraministoci dabam dabam na Israela, wanda suka haɗa da Itzatk Rabin, Shimon Perez, Benyamin Nitenyaou, Ehud Barak Ariel Sharon, sun yi haɗuwa barkatai da tawagar Palestinu bisa jagoranci Yasser Arafat.

Arafat ya kwanta dama a ƙasar France ba tare da ya ganewa idonsa  ƙasar Palestinu mai cikkaken´yanci ba.

DR Estripeau Christian na asibitin Percy, ya bayyanawa duniya wannan rashi:


Shugaban Hukumar Palestinawa Yasser Arafat ya mutu a babbar asibitin Percy Aklama ranar 11 ga watan November shekara ta 2004 a ƙarhe 3 da rabi.


Mahamud Abbas da ya gaji Yasser Arafat a shugabacin hukumar Palestinu,ya bayyana aniyarsa ta cigaba da da tattanawa da Isra´ila tare da taimakon ƙasashe da Ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, kamar Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayya Turai da kuma Amurika.

ɓangarorin sun ci gabada shirya tarruruka, taro na baya bayan nan mafi tasiri, shine wanda ya wakana a birnin Annapolis na ƙasar Amurika, bisa jagoranci shugaba Georges Bush.

Albarkacin wannan haɗuwa, shugaba Bush yayi jawabi ya na mai  cewar :

Mun haɗu a wannan mako, domin bori guda mukewa tsafi, wato mu tabbatar da girka ƙasashe biyu masu biyar tafarkin demokradiya, Isra´ila da Palestinu, wanda kuma za su maƙwabtaka da juna, cikin kwanciyar hankali da lumana.

Cimma wannan buri na buƙatara aiki wurjenjan da sadaukarwa daga ɓangarorin biyu.


Bayan shekaru 60, har yanzu babu alamun kaiwa ga tudun mun tsira ta fannin samar da zaman lahia mai ɗorewa a Isra´ila a dalili da matakin Ƙungiyar Hamas na kai hare hare da kuma ruwan bama bamai da rundunar tsaron Isr´ila ke ci gaba da yi akan Falestinawa.