1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israila ta cigaba da kai farmaki Lebanon

July 17, 2006
https://p.dw.com/p/BuqI

Israila ta cigaba da kai farmaki a rana ta shida na luguden wuta da take yi a kudancin Lebanon. Hukumomin Lebanon sun ce a ƙalla mutane 60 ne suka rasa rayukan su a farmakin jiragen sama da Israilan ta kai na baya bayan nan wanda ya kawo adadin mutanen da suka rasu ya zuwa mutane fiye da 165. Bugu da ƙari Israilan ta kuma kai hari Gaza inda ta sake yin lugude a karo na biyu a cikin mako guda a kan maáikatar harkokin waje Palasdinawa dake yankin. Israilan dai na daáwar cewa yan gwagwarmayar Hamas na amfani da maáikatar ne wajen kai mata hari. A waje guda kuma shugaban ƙungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah yace fito na fito tsakanin su da Israila yanzu aka fara. Ya baiyana hakan ne bayan hare haren rokoki guda ashirin da Hizbullah ta harba a garin Haifa dake arewacin Israila wanda ya hallaka yahudawa takwas tare da jikata wasu ashirin. P/M Israila Ehud Olmert yace Israilan zata maida martani sosai a kan waɗannan hare hare. Hizbullah ta harba rokoki fiye da dari daya zuwa cikin Israila a kwanaki biyar ɗin da suka gabata tare da kashe yahudawa goma sha biyu da jikata wasu da dama.