1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta ci-gaba da kai hare hare ta sama a Gaza dere hudu a jere

July 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bus6
Kungiyoyin Falasdinawa 3 da su ka kama wani sojan Isra´ila a Zirin gaza kwanaki 6 da suka wuce, sun gabatar da sabbin bukatu. A cikin wata sanarwa da suka bayar, sojojin sa kan na Falasdinu sun bukaci da a sako Firsinoni dubu daya da ake tsare da su a gidajen kurkukun Isra´ila kana kuma Isra´ila ta kawo karshen farmakin da take kaiwa Gaza. Ita kuma a nata bangaren kasar Yahudun Isra´ila na bukatar a sako corporal Gilad Shalit ba tare da gindaye wani sharadi ba. Jiragen saman yankin Isra´ila dai sun ci-gaba da kai hare hare dare hudu a jere a Gaza, to amma dakarun ta na kasa har yanzu suna nan sun ja daga a wajen Gaza a daidai lokacin masu shiga tsakani ke wani kokari na karshe don cimma wata masalaha. Hare hare na sama sun janyo daukewar wutar lantarki a daukacin yankin na Gaza. A yau asabar shugaban hukumar leken asirin Masar Omar Sulaiman zai isa yankin inda zai tattauna da wakilan Falasdinawa da na Isra´ila.