Isra´ila ta ce Zirin Gaza yanki ne na abokan gaba | Labarai | DW | 19.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta ce Zirin Gaza yanki ne na abokan gaba

Majalisar tsaron Isra´ila ta ayyana Zirin Gaza a matsayin wani yanki na abokan gaba. Hakan dai zai bawa Isra´ila damar katse tura wutar lantarki ruwa da kuma man fetir ga wannan yanki na Falasdinawa. Ko shakka babu wannan matakin zai dabaibaye ziyarar da sakatariyar harkokin wajen Amirka C.-Rice ta fara a yankin. A yau misis Rice ta sauka a Isra´ila don share fagen taron zaman lafiya kan yankin GTT wanda Amirka zata dauki nauyin gudanarwa. A martanin da ta mayar kungiyar Hamas wadda ke iko da Zirin na Gaza ta bayyana matakin na Isra´ila da cewa wani jan kunnen dukkan al´umar Falasdinawa ne. Wata sanarwa da Hamas ta bayar ta ce hukumar Hamas ta fara kulla wasu huldodi a fannoni da dama don hana gwamnatin Isra´ila aiwatar da wannan shiri. A jiya shugaban Hamas Isma´ila Haniya wanda har yanzu yake kiran kansa FM duk da sallamar sa da Mahmud Abbas yayi bayan da kungiyarsa ta karbe iko a Gaza, ya gana da shugabannin kungiyoyin sojojin sa kai inda ya bukace da su daina harba rokoki don hana Isra´ila daukar fansa.