Isra’ila ta ce ba ta da hannu a a tashin wata nakiya da ya kashe Falasɗinawa 8 a zirin Gaza, a ran juma’ar da ta wuce. | Labarai | DW | 14.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila ta ce ba ta da hannu a a tashin wata nakiya da ya kashe Falasɗinawa 8 a zirin Gaza, a ran juma’ar da ta wuce.

Isra’ila, ta ba da sanarwar cewa, jami’anta ba su da hannu a tashin wata nakiya a bakin teku a zirin Gaza a ran juma’ar da ta wuce, inda Falasɗinawa 8, dukkansu fararen hula daga iyali ɗaya, suka rasa rayukansu. Sanarawar ta ƙara da cewa, wata nakiyar ƙarƙashin ƙasa da Falasɗinawan suka binne ne ta yi bindiga. Amma wani ƙwararren masani a harkokin soji Marc Garlasco, mai aiki da ƙunigiyar sa ido nan kan batutuwan da suka shafi kare hakkin ɗan Adam, wato Human Rights Watch da ke da cibiyarta a birnin New York, ya sanya ƙaƙƙarfar alamar tambaya kan ikirarin da Isra’ilan ke yi, bayan ya ziyarci gun da nakiyar ta tashi.

Mutuwar fararen hular Falasɗinawan dai, ta tunzura ƙungiyar Hamas, wadda ita ce ke jagorancin Hukumar Falasɗinawa a halin yanzu, yin watsi da yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar nan da ta amince da ita a watanni 16 da suka wuce. Kai tsaye ne kuma, kusan kullum, tun daga ran nan, mayaƙanta suka fara harba rokoki kan Isra’ila.