Isra´ila ta amince Falasdinawa su yi zabe a gabashin Birnin Kudus | Labarai | DW | 15.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta amince Falasdinawa su yi zabe a gabashin Birnin Kudus

Wasu ´yan takara 3 na daga cikin ´ya´yan kungiyar Hamas da aka kame yau a gabashin Birnin Kudus wanda Isra´ila ta mayar da shi karkashin ikonta. An dai kama su ne lokacin da suka yi kokarin yin kafar ungulu da hanin da Isra´ila ta yi na yakin neman zaben a zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa da za´a yi cikin wannan wata da muke ciki. ´Yan sanda suka ce an kame mutanen ne a Birnin Kudus kusan awa daya bayan da majalisar ministocin Isra´ila ta haramtawa kungiyar Hamas yin kamfen na zaben da zai gudana a ranar wannan 25 ga watannan na janeru. Daga cikin ´yan takarar da aka kama akwai Sheikh Mohammed Abu Tir. Ko da yake majalisar ministocin Isra´ila ta amince a gudanar da zaben a yankin Larabawa dake gabashin Birnin Kudus amma ta haramtawa kungiyar Hamas tsayar da ´yan takara a zaben.