Isra´ila ta amince da yin belin wasu pirsinonin Palestinu | Labarai | DW | 17.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila ta amince da yin belin wasu pirsinonin Palestinu

Wani komitin mussamman da ya ƙunshi ministocin Isra´ila, masu angizo a kann al´amarin tsaron ƙasa, ya gudanar da taron gaggawa, domin yanke hukunci akan matakin da Praminsita Ehud Olmert ya ɗauka, na yin belin pirsinonin yaƙi Palestinawa.

Olmert ya ɗauki wannan mataki, a sakamakon ganawar da yayi da shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas jiya litinin, a birnin Ƙudus.

Shugabanin 2 ,sun yi masanyar ra´yoyi, a game da hanyoyin komawa tebrin shawarwari, da zumar kawo ƙarshen rikicin gabas ta tsakiya baki ɗaya.

Ehud OLmert, ya alƙwarata belin pirsinonin Palestinu 250 daga jimmilar Palestinawa dubu 11, da ke tsare a gidajen kurkukun Isra`ila.

Bani yahudu sun ɗauki wannan mataki da zumar ƙarawa Mahhadu Abbas ƙarfin gwiwa a rikicin da ya haɗa shi da ƙungiyar Hamas, wace a halin yanzu ke riƙe da zirin Gaza.

Mataimakin shugaban ƙungiyar FPLP ta Paletinu, Abdelkarim Malluh, na daga jerin pirsinonin 256 da komitun ministoci ya amince da belin su.

A ɗaya wajen kuma, saban mai shiga tsakanin rikicin yankin gabas ta tsakiya, wato tsofan Praministan Britania Tony Blair, ya ƙudurci bayyana saban tsarin sa, na samar da zaman lahia a yankin, ranar alhamis mai zuwa.