1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ta ɗage ƙawayar da ta yi wa gaɓar tekun Libanon

September 8, 2006
https://p.dw.com/p/Buk8

Lebanon. Hakan ya zo ne kwana daya bayan da ta dakatar da Israila ta dakatar da kawanyar da take wa gabar tekun kasar matakinta na toshe hanyoyin jiragen saman Lebanon wanda ta fara lokacinda ta kaiwa kasar hari a watan juli da ya gabata. Wannan ci gaba zai taimaka wajen hanzarta gudanar da ayyukan gyare gyare a wuraren da aka bannatar lokacin hare hare da kasashen biyu suka yi kwanaki 34 suna kaiwa juna, kamar yadda aka ji daga bakin Miri Eisin mai magana da yawun prainministan Israila, Ehud Olmert. Kakakin hafsan sojin UNIFIL dake da alhakin wanzar da zaman lafiya a Lebanon, yace rundunar sojin ruwa a karkashin jagorancin kasar Italiya sun dauki nauyin aikin santiri a gabar tekun Lebanon daga hannun Israila. Israila ta dauki matakai na toshe hanyoyin jiragen sama da na ruwa a kasar Lebanon a lokacinda ta kaiwa kasar hari a watan juli da ya gabata. A nasa bangaren kuma, ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya fadawa tashar telebijin ta kasar cewar itama Jamus zata bada nata taimakon da zarar sharrudan yin haka sun cika.