Isra´ila na wani shiri a ɓoye don lalata shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 07.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila na wani shiri a ɓoye don lalata shirin nukiliyar Iran

Jaridar Sunday Times ta Birtaniya ta rawaito cewa Isra´ila ta tsara wani shiri a asurce da nufin lalata tashoshin sarrafa sinadaran Uranium a Iran ta amfani da wasu makaman nukiliya. Jaridar mai fita a kowane mako ta rawaito wasu majiyoyin sojin Isra´ila na cewa an horas da wasu rundunoni biyu na sojin saman kasar ta bani Yahudu ta yadda zasu yi amfani da makaman a bugu daya. Rahoton ya kara da cewa za´a yi amfani da wannan shiri ne idan aka kawad da yiwuwar amfani da matakan soji da aka saba. Ana iya kallon fallasa wannan shiri da wata niya ta matsawa Teheran lamba ta dakatzar da shirinta na nukiliya. Shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nejad ya sha yin kira da a share Isra´ila daga doron kasa.