Isra´ila na shirin kafa wani yankin tsaro a kewayen Zirin Gaza | Labarai | DW | 24.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila na shirin kafa wani yankin tsaro a kewayen Zirin Gaza

Isra´ila ta ce tana nazari game da gina wani yankin tsaro don hana Falasdinawa kai hare haren makamai masu linzami daga arewacin Zirin Gaza. Kamar yadda tashar telebijin din Isra´ila ta rawaito, sojojin kasar zasu kafa wani yanki da ba na kowa ba a kusa da iyakar Zirin na Gaza, inda zasu rika harbe duk wanda ya kuskure ya shiga wannan yanki na tsaro. Tashar ta kara da cewa wannan yanki zai zagaye unguwannin yahudawa ´yan kama wuri zauna da aka janye daga Gaza a cikin watannin agusta da satumba da suka gabata.