Isra´ila na ci-gaba da matsa kaimi a Zirin Gaza | Labarai | DW | 08.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila na ci-gaba da matsa kaimi a Zirin Gaza

Rahotanni daga yankin Falasdinawa sun ce daruruwan sojojin Isra´ila sun kutsa cikin birnin Gaza a jiya daddare. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun rawaito cewar tankokin yaki da jiragen saman yaki masu saukar ungulu suka dafawa sojojin baya. A wani kazamin fada da aka gwabaza a kusa da yankin Karni an kashe Bafalasdine daya. Jami´an tsaron Falasdinawa da na asibiti sun ce akalla mutane biyu sun samu raunuka lokacin da sojin saman Isra´ila suka harba makamai masu linzami akan gungun sojojin sa kai. A halin da ake ciki babban sakataren MDD Kofi Annan ya sake yin kira ga sassan biyu dake rikici da juna da su tsagaita wuta don hana aukuwar wani bala´i. A cikin wata sanarwa da ya bayar yayin ziyarar da yake kawowa birnin Berlin Annan ya ce dole ne Isra´ila ta dakatar da matakan sojin da take dauka nan take sannan su kuma a nasu bangaren Falasdinawa su daina harba rokoki cikin Isra´ila kana kuma su saki sojinta da suka yi garkuwa da shi ba da bata lokaci ba.