Israila na ci gaba da luguden wuta a Lebanon | Labarai | DW | 18.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila na ci gaba da luguden wuta a Lebanon

Jiragen yakin Israila sunci gaba da kai hare hare kan kudancin Beirut daga cikin daren jiya ya zuwa safiyar yau talata.

Rahotanni sunce an ji fashewar bama bamai da suka girgiza birnin Beirut,hakazalika jiragen yakin na Israila sun kai hari akan yankunan da jamaa suke zaune a birnin Baalbek dake gabashin Lebanon da safiyar yau din nan.

Baki dai na ci gaba da tserewa daga kasar ta Lebanon,ciki har da yan kasar Jamus,wadanda yawan su ya kai 400 da suka bar Lebanon zuwa kasar Syria cikin bus bus.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeire yace mafi yawa daga cikinsu sun iso Dusselldorf.

Gwamnatin jamus din tace akwai akalla wasu Jamusawa 2000 da suka saura a kasar ta Lebanon.