Israila na ci gaba da kai hari zirin Gaza | Labarai | DW | 29.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila na ci gaba da kai hari zirin Gaza

Kasar Israila tana ci gaba kai hare hare ta sama zuwa zirin Gaza bayan waadin da ta dibawa Palasdinawa su bar yankin tsaro inda bayan kai hare hare da roket ya cika.

Wani ministan Israilan kuma yaki ya baiyana tsawon lokaci da Israilan zata dauka na ci gaba da kaiwa hare harensu a arewacin zirin Gaza.

Mataimakin Firimiya Ehud Olmert,yace Israila zata ci gaba da hari da take kaiwa muddin dai ana ci gaba da kai mata hari da makaman roka.

A wani labarin kuma rahotanni daga Israilan sunce roket da aka harba mata daga kudancin kasar Lebanon kirar kasar Rasha ne da ta sayarwa kasar Syria