Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren bamabamai a Lebanon. | Labarai | DW | 19.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra’ila na ci gaba da kai hare-haren bamabamai a Lebanon.

Isra’ilan dai na ci gaba da kai hare-haren da ta fara tun kwanaki 7 da suka wuce a kann Lebanon. Rahotannin baya-bayan nan da muka samu sun ce, wani rukunin dakarun Isra’ilan ya shiga kudancin Lebanon don kai hari kan ramin kurar ’yan ƙungiyar Hizbullahi. Wani kakakin rundunar sojin ƙasar Bani Yahudun ya ce wannan kutsawar dai ta wucin gadi ne. A ɗaya ɓangaren kuma, jiragen saman yaƙin Isra’ilan sun ci gaqba da kai hare-haren bamabamai a wasu wurare kusa da filin jirgin saman Beirut da kuma kudancin Lebanon, a rana ta 8, ta ɗaukin da Isra’ilan ta fara a ƙasar. Rahotanni sun ce jiragen saman sun kuma lalata wata gada a garin Sidon wanda shi ma ke kudancin Lebanon ɗin.