1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra’ila na ci gaba da kai farmaki a ƙasar Lebanon.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bupb

A rana ta goma sha biyu a jere, Isra’ila na ci gaba da farmakinta a ƙasar Lebanon, inda da sanyin safiyar yau, jiragen saman yaƙinta suka kai hare-haren bamabamai kan wasu guraba a birnin Beirut da kuma garin Sidon da ke kudancin ƙasar. Kafofin yaɗa labarai dai sun ce an ji amon tashin bamabamai a wasu yankuna na Beirut, sa’annan a Sidon kuma, jiragen Isra’ilan sun ragargaza wani masallaci da farfajiyarsa. Wani rukunin dakarun Isra’ilan kuma ya kutsa cikin ƙauyen Maroun al-Ras, inda rahotanni suka ce a halin yanzu, ƙauyen na hannunsu. Har ila yau dai, a arewcin Beirut kuma, jiragen Isra’ilan sun lalata tashoshin yaɗa labaran gidajen talabijin na ƙasar ta Lebanon da kuma wata hasumiyar sadaswa ta tarho na salula, abin da ya janyo katsewar hanyoyin buga waya da salulan a duk arewacin ƙasar.

Kawo yanzu dai, alƙaluma na nuna cewa, a wannan farmakin da Isra’ila ta kai a Lebanon wai don gurgunta ƙungiyar Hizbullahi, mutane ɗari 3 da 35 sun rasa rayukansu, mafi yawansu kuma fararen hula ne. A ɗaya ɓangaren kuma, rokokin da ’yan Hizbullahin suka yi ta harbawa zuwa Isra’ila, ya janyo asarar rayukan mutane 35, ’yan ƙasar bani Yahudun.