1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Kotu ta soke shirin fidda 'yan gudun hijira

Abdul-raheem Hassan
March 15, 2018

Kotun kolin ta ba wa gwamnatin Isra'ila wa'adin zuwa 26 ga Watan Maris da ta gabatar da karin hujjoji kan matakin ta na neman tisa keyar 'yan Afirka da ke gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2uPYm
Isreal illegale Immigration
Hoto: picture-alliance/dpa

Kotun koli a kasar Isra'ila ta yanke hukuncin haramta shirin gwamnati mai cike a takaddama na maido da dubban 'yan Afirka da ke neman mafaka a kasar. Ma'aikatar harkokin cikin gidan Isra'ila ta ce akwai mata da kananan yara dubu 42 da dokar korar ba ta hau kansu ba.

A watan Janairun shekara ta 2018 ne Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba wa 'yan gudun hijira mafi akasari wadanda suka fito daga kasashen Afirka zuwa Isra'ila ba bisa ka'ida ba zabin ficewa kasar cikin girma da arziki ko da karfin tuwo. Sai dai wannan mataki ya fuskanci suka daga hukumomin kare hakin bil'adama na Majalisar Dinkin Duniya da sauran kungiyoyin fararen hula da ke rajin kare hakkin dan Adam a duniya.