1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila da Hisbollah na yiwa juna barin wuta

A ci-gaba da fafatawa kuwa mayakan Hisbollah a kudancin Libanon sun sake harba rokoki zuwa arewacin Isra´ila, inda ta halaka mutum 3 sannan wasu biyar suka jikata a kauyen Arab Al-Aramshe dake kan iyaka da Isra´ila. Yanzu haka dai fararen hular Isra´ila 33 ne suka rasu sakamakon rokokin Hisbollah tun fara wannan rikici sama da makonni 3 da suka wuce. Da farko jami´an sojin Isra´ila sun ce sun lalata rabin rokoki masu cin dogon zango na Hisbollah. A kuma halin da ake ciki Isra´ila ta ce ta kai samame cikin wani gida dake birnin Tyre inda ta kashe sojojin sa kai da dama yayin da sojojin ta 8 suka samu rauni. Gidan telebijin Hisbollah ya rawaito cewa mayakan ta sun fatattakin sojojin Isra´ilan.