1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila da Hamas na ci-gaba da kaiwa juna hare hare

Isra´ila da mayakan kungiyar Hamas sun ci-gaba da musayar wuta inda Isra´ila ta yi ta kai farmaki ta sama yayin da Hamas ta yi harba rokoki. Rahotanni sun nunar da cewa an harba rokoki akalla 8 cikin Isra´ila. A jiya wani bayahude ya rasa ransa a wani harin roka da aka kai kan motarsa a garin Sderot dake kan iyaka tsakanin Isra´ila da Zirin Gaza. Su kuma a na su bangaren jiragen saman yakin Isra´ila sun yi ta harba makamai masu linzami akan sansanonin mayakan Hamas dake Zirin Gaza. Alkalumman da Falasdinawa suka bayar sun yi nuni da cewa an halaka akalla mutane 48 tun bayan fara kai farmaki ta sama a Zirin Gaza kimanin makonni biyu da suka wuce.