1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra´ila ba zata kaddamar da farmaki na gama gari a Zirin Gaza ba

November 1, 2006
https://p.dw.com/p/Budg
Majalisar tsaron Isra´ila ta yi fatali da ba da wani umarni na kai gagarumin farmakin sojin kasa a Zirin Gaza. Ofishin FM Ehud Olmert ya ce duk da haka za´a ci-gaba da farmakin sojin da aka fara yau laraba a arewacin Zirin na Gaza da nufin hana Falasdinawa harba rokoki cikin Isra´ila. A jiya daddare an kashe Falasdinawa 6 sannan aka jikata 35 a wani samame da sojojin Bani Yahudu suka kai a garin Beit Hanun dake arewacin Gaza. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce sojojin Isra´ila dake samun kariya daga tankokin yaki sun kwace garin sannan suka toshe kofar shiga babban asibitin garin. Wani kakakin sojin Isra´ila ya tabbatar da cewa ana wani gagarumin aikin soji a yankin kuma wasu hare hare biyu ta sama sun afkawa gungun sojojin sa kai su 30. A wani labarin kuma an kashe sojin Isra´ila daya a Zirin Gaza, inda Isra´ila ta kaddamar da wani famakin soji cikin dare.