Israila amincewa Palasdinawa yekuwar zabe a Qudus | Labarai | DW | 09.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israila amincewa Palasdinawa yekuwar zabe a Qudus

Militärputsch in Mauretanien

Militärputsch in Mauretanien

Kasar Israila tace zata baiwa yan takarar zaben majalisar dokokin palasdinu damar yekuwar neman zabe a gabashin Qudus muddin dai ba membobin kungiyoyin sa kai bane.

Ministan kula da tsaron cikin gida na Israila Gideon Ezra yace dukkan wadanda suke bukatar kanfe kamata yai su gagguata mika takardun yin hakan ga rundunar yan sanda ta birnin Qudus,kafin amince musu yekuwar neman zaben sai dai ministan bai baiyana ko Israila zata amincewa Palasdinawan yankin jefa kuriarsu ba a zaben ranar 25 ga watan janairu.