Israela zata fara bincikar wasu sojin kasar | Labarai | DW | 20.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israela zata fara bincikar wasu sojin kasar

Tururuwa akan Danyatsa

Tururuwa akan Danyatsa

Dakarun sojin Israela na shirin fara binciken zargin da akewa wasu sojin kasar, na amfani da tagwayen bama bamai a lokacin yaki tsakanin kasar da Lebanon.

A cewar rahotanni daga kasar, kafin fara yakin , shugaban rundunar sojin Kasar wato Laftanar Janar Dan Hulutz ya hana ayi amfani da irin wadannan bama bamai.

An dai gano cewa wasu daga cikin sojin kasar, sunyi amfani da irin wadannan bama bamai ne, a lokacin wani bincike da aka gudanar.

Bugu da kari a waje daya kuma, hukumar kare hakkin bil adama ta human Rights Watch ta zargi sojin kasar ta Israela da harba irin wadan nan bama bamai cikin cunkosun jama´a a lokacin wannan yaki.

A dai karshen wannan yaki, an kiyasta cewa mutane 20 ne suka rugamu gidan gaskiya wasu kuma 70 suka jikkata, a sakamakon amfani da irin wadan nan tagwayen bama baman.