Israela ta kashe wasu Palasdinawa | Labarai | DW | 01.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israela ta kashe wasu Palasdinawa

Palastin/Israeal

Wasu Palasdinawa biyu sun rasa rayukansu wani guda daya kuma ya sami raunka a wani harin makamai da sojan Israela suka harba a kusa da garin Beit Lahiya dake arewacin Gaza.

Kakakin sojan Israela ta ce sojojin na Israela sun kai harinne akan wasu yan gwagwarmayar palasdinwa da suka tsinkaya sun dana wani makami suna shirin ,harbawa kan Israelan,bayan an harba wasu biyu da basu haifar da wani lahani ba.

Jamian tsaron palasdinu sun tabbatar da cewa an harba wani makami daga yankin da mutanen suke amma basu da tabbas ko mutanen da Israelan ta kashe su suka harba shi ba.

A farkon makon da ya wuce ne dai Israelan ta kebe wani yanki a arewacin Gaza da ta haramtawa palasdinawa shiga cikinsa saboda martanin hare haren makaman da suke harba mata ta yankin.

Hare haren da Israealan take kaiwa Palasdinawan da martanin da yan gwagwarmayar ke maidawa dai sun gurgunta yar yarjejeniyar zaman lafiyar da yan gwagwarmyar palasdiwan suka amince da ita a farkon shekarar data kare,inda kungiyoyin palasdiwan ciki har da Hamas suka ce daga ranar daya ga watan janairun nan, wato yau ba za su sake girmama wannan yarjejeniya ba.