Israela ta kara kai sabbin hare hare Lebanon | Labarai | DW | 04.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israela ta kara kai sabbin hare hare Lebanon

Kafafen yada labaru sun rawaito cewa, jami´an Mdd na ci gaba da tattaunawa a game da samo bakin zaren warware rikicin dake tsakanin Israela da kuma kungiyyar Hizbullah.

Ci gaba da wannan tattaunawa dai tazo ne a dai dai lokacin, da dakarun sojin Israela suka kai wasu munanan hare hare ta jiragen sama a kudu da kuma arewacin birnin Beirut dake kasar ta Lebanon.

Kamar kullum dai rahotanni sun nunar da cewa anyi asarar rayukan fararen hula da dama a waje daya kuma da jikkata wasu, a sakamakon wadan nan sabbin hare hare.

Ya zuwa yanzu dai mahukuntan na Israela, sun shaidar da cewa ana kai wadannan hare hare ne da zummar kwato yankunan dake karkashin ikon kungiyyar ta Hizbulla.