1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Israela ta kara kai hari a kudancin Lebanon

July 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bup0

Dakarun sojin Israela sun kara kai wasu manya manyan hare hare a kudancin kasar Labanon, a wani yunkuri da suka kira na kokarin dakile aiyukan yan kungiyyar Hizbulla.

Rahotanni sun shaidar da cewa sojin na Israela sun yi amfani ne da jiragen sama da kuma motoci kirar igwa masu aman wuta a yayin kai wadan nan hare hare.

An dai bayyana wadan nan hare hare na yau a matsayin mafi muni a tsawon kwanaki goma sha shidda da aka shafe ana musayar wuta, a tsakanin dakarun sojin na Israela da kuma mambobin kungiyyar ta Hizbullah.

Wannan hari dai a cewar rahotanni ya biyo bayan kisan wasu dakarun sojin Israela tara ne da akayi a wani dauki ba dadi a tsakanin su da dakarun kungiyyar Hizbulla a jiya laraba.

A tsawon wannan lokaci dai an bayyana cewa, mutane 423 ne suka rasa rayukan su a kasar ta Labanon, kana a waje daya kuma Israela tayi asarar rayuka 52.

A dai wani lokaci ne a yau din nan ake sa ran jami´an gudanarwar kasar ta Israela zasu gudanar da taro, wanda a lokacin ake sa ran zasu dauki matakin kara kai mi na ci gaba da kai irin wadan nan hare hare ko kuma akasin haka.