Israela ta kai sabbin hare hare a zirin Gaza | Labarai | DW | 27.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Israela ta kai sabbin hare hare a zirin Gaza

Jiragen Israela masu saukar ungulu sun kai wasu hare haren rokoki a arewacin zirin Gaza da jijjibin safiyar yau talata.

Wani bapalasdine daya ganewa idon sa ya shaidar da cewa daya daga cikin rokokin ta sauka ne a cikin wani gini mallakar jamiyyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas,daya rokar kuwa ta sauka ne a wani guri na daban sabanin inda aka nufi data lalata.

Ya zuwa yanzu dai babu rahoton rasa rai ko kuma jikkata,sakamakon wadannan rokoki da aka harbo izuwa zirin na gaza.