1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Iskar tashin hankali na ci gaba da kadawa a Faransa

Tun kwanaki 11 ke nan da ake ta ci gaba da arangama tsakanin jami'an tsaro da matasa a kasar Faransa. Matasan, haifaffun kasar, amma masu asali ko kuma iyaye baki, suna nuna bacin ransu ne ga irin halin da suke ciki, da kuma abin da suke ganin kamar wariya ce ake nuna musu.

Matasa masu zanga-zanga suna jifar `yan sanda da duwatsu a karawar da suka yi da su a birnin Paris.

Matasa masu zanga-zanga suna jifar `yan sanda da duwatsu a karawar da suka yi da su a birnin Paris.

Jigon kasar Faransa dai, shi ne `yanci, da `yan uwantaka da kuma adalci. Amma a cikin kwanaki 11 nan da suka wuce, ba a ga alamun wannan jigon ba. A ko wane dare na wadannan kwanakin, sai matasa sun yi ta arangama da `yan sanda, wadanda suke ta kokkona motoci, bisa wasu rahotannin ma, suke bude wa jami’an tsaron wuta.

Abin da tambaya anan shi ne, wai kasar ta Faransa tana nuna alamar gazawa ne ? Duk gwamnatocin kasar masu bin ra’ayoyi daban-daban, sun sha gabatad da shirye-shirye iri-iri don shawo kan matsalar ta unguwannin kewayen birnin Paris, inda a galibi matasan da iyayensu baki ne suka fi zama a can. Amma har ila yau, babu wani muhimmin sakamakon da aka cim ma. Da can tsohuwar gwamnatin Faransan ta jam’iyyar Socialist, ta gabatad da wani shiri ne na tuntubar juna, inda a ko yaushe tawagar `yan sanda ke saduwa da wakilan matasan don tattauna matsalolin da suke huskanta a unguwanninsu. Amma tun da aka sake gwmantin ne al’amura suka fara tabarbarewa. Minista harkokin cikin gida na yanzu, Nicolas Sarkozy, ya fi gwammacewa ne da bin tafarkin doka da oda. Amma wannan matakin da za a iya kwatanta shi da mulkin muzgunawa da ministan ya dauka, bai janyo wata fa’ida ba. A daura da haka ma, sai ga shi, yau, bayan kwanaki 11 na arangamar da matasan suka dinga yi da `yan sanda, an yi ta samun karin yawan motocin da aka kokkona, sa’annan rikicin kuma, ya yadu zuwa wasu yankuna da jihohin kasar.

A halin yanzu dai, matasan ba sa nuna alamun sassauci a kan matsayinsu, duk da bayanin da Firamiyan kasar ya yi na gabatad da wani shiri na gaggawa.

Da can dai, Faransan ce ake gani kamar wata jagora a nan Turai, wajen magance matsalar sajewar al’ummomi daban-daban da ke zaune a kasar. Za a iya ganin hakan ne dai, musamman a lokacin gasar cin kofin kwallon kafar nan ta duniya da aka yi a shekaru 7 da suka wuce a Faransan, inda kungiyarta ce ta cinye kofin. A wannan lokacin, kungiyar ta kunshi `yan wasa matasa ne, wadanda a galibi `ya`yan baki ne da suka yi kaura zuwa Faransan.

Amma yanzu iskar wannan abin da Faransan ke alfahari da shi, ya sake kadawa a zuwa wata shiyya daban kuma. Masharhanta da dama dai na bayyana cewa, bai wa baki Fasfotunan Faransa kawai, ba shi ne zai magance matsalolin da suke huskanta ba, musamman wajen samun aikin yi da dai sauransu. A unguwannin da suka fi rinjayin mazauna baki da `ya`yansu da suka haifa a nan kuma, za a lura da cewa, duk matsugunan suna cikin wani mummunan hali ne da ke bukatar gyara kai tsaye.

Babu dai wanda ake zargi yanzu da fifita wutar rikicin, kamar ministan harkokin cikin gidan kasar Nicolas Sarkozy, wanda jama’a da dama ke ganin wasu kalamun da ya yi na cewa, za a tsabtata unguwannin kewayen Paris daga `yan daba, wato tsokana ce ga mazauna yankunan.

Abin damuwa dai ga sauran kasashen Turai a halin yanzu shi ne, fargabar da suke yi ta cewa, wannan rikicin da ya fara a Faransa, zai yadu zuwa sauran kasashen nahiyar, inda a nan ma, ake da dimbin yawan matasa, `ya`yan bakin da suka yi kaura tun shekaru da dama da suka wuce.

Har ila yau kuwa, nahiyar ba ta samo bakin zaren warware wannan matsalar ba tukuna. Amma a zahiri, su `ya`yan bakin, wadanda a halin yanzu, ba su san ma inda za su mai da alkiblarsu ba, su ne za su kasance manyan gobe.

 • Kwanan wata 07.11.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUW
 • Kwanan wata 07.11.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvUW