1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iskar Sidr na ci gaba da mummunan aiki a Bangladesh

Jami´an Gwamnati a Bangladesh sun ce mutane a ƙasar na ci gaba da rasa rayukansu, a sakamakon Iskar nan mai ƙarfi ta Sidr. Iskar dake tafe da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, a yanzu haka tayi ajalin mutane sama da dubu ɗaya.Rahotanni sun ce yankin Kudu maso yammacin ƙasar ne wannan bala´i, ya fi yiwa mummunan ta´adi..Ayyukan agaji a wannan yanki, a yanzu haka na fuskantar tsaiko, a sabili da ambaliyar ruwa data mamaye yankin.Tuni dai Ƙungiyyar Tarayyar Turai tayi alkawarin tallafawa ƙasar da Yuro miliyan ɗaya da ɗigo shidda,don tallafawa waɗanda wannan bala´i ya afkawa.