Iska mai karfin gaske na kara baza wutar daji a California | Labarai | DW | 23.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iska mai karfin gaske na kara baza wutar daji a California

Zafin yanayi da iska mai karfi suna kara baza wutar daji a kudancin jihar california a kasar Amurka.An bukaci mutane fiye da 300,000 da su bar gidajensu.Wannan wuta dai ta kona gidaje kusan 700 tare da kona fiye da hecta 250,000 na filaye.rahotanni sunce wutar tana bazuwa cikin gaguawa ta ibda dole aka kwashe jamaar da aka tura otel otel don neman mafaka.Jamian kashe gobara fiye da 5,600 suke kokarin shawo kann wannan wuta