ISAR′ILA TA YI WA SHUGABAN KUNGIYAR HAMAS SHEIKH YASSIN KISAN GILLA | Siyasa | DW | 22.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ISAR'ILA TA YI WA SHUGABAN KUNGIYAR HAMAS SHEIKH YASSIN KISAN GILLA

Dakarun Isra'ila sun yi wa shugaban kungiyar nan ta Hamas, Sheikh Yassin kisan gilla, a wani harin jiragen sama masu saukar ungulun da suka kai masa a zirin Gaza. Wata kafar gwamnatin Isra'ilan ta ce Firamiya Ariel Sharon da kansa ne ya ba da umarnin kashe Sheikh Yassin din. A nata bangaren, kungiyar ta Hamas ta lashi takobin mai da martani da kashe darurukan Yahudawa.

Sheikh Ahmed Yassin, shugaban kungiyar Hamas da dakarun Isra'ila sukka yi wa kisan gilla a birnin Gaza.

Sheikh Ahmed Yassin, shugaban kungiyar Hamas da dakarun Isra'ila sukka yi wa kisan gilla a birnin Gaza.

Babu shakka, gwamnatin Ariel Sharon na amfani da yakin nemna zaben da ake yi a Amirka ne wajen cin karensa babu babbaka. Ta hakan ne kuwa mahukuntan Isra’ilan suka ba da umarnin kashe shugabannin kungiyar Hamas daya bayan daya, abin da ya kai kololuwarsa da kisan gillar da dakarun Isra’ilan suka yi wa Sheikh Ahmed Yassin, shugaban kungiyar islaman nan ta Hamas. A da’irar gwamnatin Isra’ilan dai, ana kwatanta Sheikh Yassin ne tamkar "Bin Laden din Isra’ila". Gurin mahukuntan Isra’ilan ne dai, su danganta arangamar da kasar ke yi da Falasdinawa da abin da Amirka ke kira yaki da ta’addanci, su kuma kawo su a matsayi daya. Amma nasarar da suke fatar samu, ta bayyana wa gamayyar kasa da kasa cewa, a matsayi daya suke da mahukuntan birnin Washington a fafutukar yakan tadaddanci, ba ta da tabbas.

Har ila yau dai, shugaba Bush na Amirka na cikin wadanda ke kare Ariel Sharon da kuma daure masa gindi. Amma a nan ma, a wannan lokaci na yakin neman zabe a Amirkan, da kuma yadda al’amura ke ta tabarbare wa Amirkan a Iraqi, mai yiwuwa shugaba Bush ya sake salonsa.

A zahiri dai, da kamata ya yi masu tsara manufofin siyasar Amirka su daina kare Sharon da kuma ba shi daurin gindi, kafin ma al’amura su tabarbare. Yin haklan dai zai fi janyo wa Isra’ilan fa’ida a wanzuwarta tamkar kasa mai cin gashin kanta. Duk da kasancewar Yassin shugaban kungiyar ta Hamas, wanda kuma a wasu lokuta, yake bayyana gamsuwarsa a fili da hare-haren kunan bakin waken da ake kai wa Isra’ila, amma ba shi ne ke tura ‘yan kunan bakin waken zuwa ta da bamabamai a Isra’ilan ba. Shi dai Yassin, ba shugaba yake ga kungiyar Hamas din kawai ba. Wasu Falasdinawan da ba su da wata jibinta da Hamas din ma na ganinsa ne kamar shugaba mai daukaka gare su. Sabili da haka, kisan gillar da Isra’ilan ta yi masa, babu abin da zai janyo, sai habaka tashe-tahsen hankullan da ake samu tsakanin kasar Yahudun da Falasdinawa. Tsohon ministan shari’a na Isra’ilan Yossi Beilins, yana nuna matukar shakkunsa ga yiwuwar cim ma nasarar gwamnatin Sharon da daukar wannan matakin. Fargabarsa dai ita ce, wannan daukin zai haifad da wani mummunan sakamako, inda dimbin yawan `yan kasar bani Yahudun za su rasa rayukansu.

Tun da Falasdinawan suka fara borensu na " Al-Aqsa-Intifada" dai, Yahudawa fiye da dari 4 ne suka rasa rayukansu. Amma Isra’ilan ta ki neman sasanta rikicin, tana mai da martani ne ko yaushe da kisan wasu Falasdinawan, abin da kuma ke angaza karin yawan Falasdinawan su dinga bin manufofin masu tsatsaurar ra’ayi. Ta hakan ne dai aka yi ta samun hauhawar tsamari a yankin.

Matakan da Isra’ilan ke dauka yanzu dai, ba su da wani tushe a dokokin kasa da kasa. Sabili da haka ne kuwa, za ta yi ta kara samun suka daga gamayyar kasa da kasar. Yawan masu yi mata saniyar ware kuma, zai ta kara habaka.

Kisan gillar da aka yi wa Shiekh Yassin dai, na cikin tsarin da Isra’ilan ta shirya kammalawa ne, kafin ta fice daga zirin Gazan, kamar yadda Sharon ya bayyanar. Amma ficewarta a yanzu zai yi matukar wuya, saboda wannan danyen aikin da dakarunta suka gudanar yau, na yi wa daya ddaga cikin muhimman shugabannin al’umman Falasdinu kisan gilla.

 • Kwanan wata 22.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlB
 • Kwanan wata 22.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlB