IS ta halaka ′yan Shi′a kimanin 70 a Iraki | Labarai | DW | 24.11.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

IS ta halaka 'yan Shi'a kimanin 70 a Iraki

A Iraki Musulmi 'yan Shi'a akalla 70 ne suka halaka a cikin wani harin ta'addanci da aka kai da wata mota wacce aka dana wa bam a wannan Alhamis a wani kauye mai suna Chomali da ke a nisan kilomita 120 da birnin Tehran. 

Motar wacce ke shake da sinadarin Nitrat ta tarwatse a tsakiyar wasu motocin safa na bas-bas wadanda ke shake da mabiya mazhabin Shi'a wadanda ke dawowa daga birnin Karbala'a inda suka halarci taron 40 na kammala zaman makokin tunawa da kisan Imam Husseini jikan Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi wanda sojojin gwamnatin banu Umayya ta Yazidu suka yi wa kisan gilla a shekara ta 680.  Tuni dai Kungiyar IS ta dauki alhakin wannan hari wanda ta ce wani mayakinta ne dan kunar bakin wake ya kai shi. Musulmi mabiya tafarkin Shi'a miliyan 17 zuwa miliyan 20 ne dai suka halarci taron makokin a birnin na Karbala a ranar Litinin da ta gabata.