1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS na gap ga sake kwace birnin Palmyre a Siriya

Gazali Abdou TasawaMay 12, 2016

Masu aiko da rahotanni sun ce yanzu haka mayakan IS sun yi wa birnin na Palmyre kofar raggo, mako daya bayan da sojojin gwamnatin Siriya da na Rasha suka yi bikin murnar karbo shi daga hannun Kungiar ta IS.

https://p.dw.com/p/1Im6J
Syrien Altertum Gebäude
Hoto: globe-trotter/Fotolia

Rahotanni daga Siriya na cewa mayakan Kungiyar IS sun samu gagarumar nasara kan sojojin Bashar al-Assad a kusa da birnin palmyre, birnin da suke gap da sake karbe iko da shi, bayan da sojojin gwamnatin suka kwace shi daga hannunsu a ranar 27 ga watan Maris din da ya gabata.

Kawancan kungiyoyin kare hakin dan Adam na kasar ta Siriya wato OSDH ya ce a ranar Talatar da ta gabata ce mayakan Kungiyar ta IS suka yi nasarar kwace babbar hanyar da ta raba biranen Homs da Palmyre.

Masu aiko da rahotanni sun ce yanzu haka mayakan Kungiyar ta IS sun yi wa birnin na Palmyre kofar raggo, mako daya bayan da sojojin gwamnatin Siriya da na Rasha suka yi bikin murnar karbo shi daga hannun Kungiyar ta IS.

Karbe iko da wannan babbar hanya ta tsakanin wadannan birane biyu ita ce nasara mafi girma da mayakan Kungiyar ta IS suka samu tun bayan da sojojin gwamnati suka yi nasarar karbe ikon da birnin na Palmyre wanda ke zama birnin tarihi.