1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iraqi za ta karɓi ragamar tsaron a ƙarshen shekara

October 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buep

Mukaddashin P/M Iraqi Barham Saleh yace nan da karshen wannan shekarar da muke ciki, gwamnatin Iraqin za ta karbi ragamar gudanarwar ta shaánin tsaro a rabin gundumomin goma sha takwas dake fadin kasar duk da karuwar tarzoma dake cigaba da wakana a kasar. A bayan ganawar sa da P/M Britaniya Tony Blair a birnin London, Barham Saleh yace babu shakka abin damuwa ne yadda ake samun karuwar tarzoma da tabarbarewar shaánin tsaro a kasar Iraqi, yace to amma wajibi ne gwamnatin ta nuna zata iya tabbatar da doka da oda. Yace suna bukatar tallafi da kwarin gwiwa daga gamaiyar kasa da kasa, duk da cewa yan Iraqin su ne za su zamo ja gaba. Mukaddashin P/M yace sannu a hankali, ya zuwa farkon shekara mai kamawa dakarun Iraqi za su karbi ragamar tsaron larduna bakwai zuwa takwas daga cikin gudumomi goma sha takwas a fadin kasar. A nasa bangaren P/M Tony Blair yace Britaniya za ta tsaya tsayin daka tare da cigaba da bada gudunmawa a Iraqi.