1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran zata yi sassauci kan rikicin Atom

February 3, 2010

Kasar Iran tace zata amince da bukatun kasashen yamma a rikicin su game da tashoshin Atom

https://p.dw.com/p/LrVV
Jakadan Iran a hukumar Atom ta duniyaHoto: AP

A lokacin jawabin sa ga al'ummar Amerika a kwanakin baya, shugaba Barack Obama ya gabatarda kalamomi masu karfi zuwa ga kasar Iran. Yace:

Tun da shike shugabannin dake mulki a Iran suna ci gaba da kunnen kashi da nauyin dake kansu gaba daya na dokokin kasda da kasa,, bai kamata suyi shakkar cewar gwmnati a Teheran zata dandana kudar ta game da haka ba.

Wannan sako na Obama, da alamu yanzu dai ya cimma wadanda aka yi shi domin su a Iran. Shugaba Mahmud Ahmedinejad ya sanar a wani jawabi ta gidan television na kasar cewar yana da shirin canza ra'ayin sa domin cimma bukatun kasashen yamma kan batun na tashoshin atom. To sai dai Amerika tafi son ganin ya aiwatard a hakan ne a zahiri, amma ba ta jawabnan fatar-baka ba.

Gwamnatin Iran tana keta dokokin duniya, wadanda ko wace kasa ya kamata ta mutunta su, inji shugaban Amerika Barack Obama.

Gwamnatin Obama ta zargi Iran da cewar tana kin kula da kudorin majalisar dinkin duniya, ta hanyar ci gaba da giggina tashoshin nuclear na karkashin kasa.

Obama ya bada shawarar cewar Iran ta kai misalin kilogram 1200 na sinadarin uranium zuwa Faransa da Rasha inda za'a tace shi, yadda zata yi amfani da wnanan sinadari a tashoshin nuclear na samnun makamashi ne kawai. Amerikan ta kuma dagewa Iran takunkumin da ya hana samun tuntubar juna tsakanin kasashen biyu na tsawon fiye da shekaru talatin, inda a karon farko a bara kasashen na Iran da Amerika suka zauna kan teburin shawarwari daya, amma hakan bai amfana komai ba.

Babban kwamandan askarawan Amerika a yankin Gulf, David Petraeus yake cewa:

Shugaba Obama da ministan tsaro da ni kaina, duka mun daidaita kan cewar wajibi ne a duba dukkanin hanyoyi na daidaitawa.

Babu shakka kuwa, amfani da karfin soja yana daga cikin wadannan hanyoyi da ake iya duba su, inji Admiral Mike Mullan, na rundunar jsojan ruwa na Amerika a wnanan yanki.

Sakataren tsaron Amerika, Robert Gates yayi barazanar cewar:

Idan ma aka yi watsi da kokarin da Iran take yi na daurawa kanta damarar makaman nuclear, makaman da take dasu ma wadanda ba ma nuclear ba, suma kansu sun isa haddasa damuwa.

Sakataren tsaron na Amerika ya baiyana imanin cewar yiwa Iran sassaucci ba shine abin da ya dace ba, saboda kasar bata fahimtar komai sai barazanar nuna karfi a kanta. Saboda hjaka ne yace a yankin na Gulf an kara karfafa hadin kan soja da tsaro tare da kawayen Amerika.

Jaridar New York Times tace taji labarin cewar Amerika tana giggina matakan kariya, ta amfani da rokokin Patriot a teku da kuma a kasa a Katar da taraiyar daular Larabawa da Kuweit, tana kuma taimakawa Saudi Arabia a game da horad da sopjoji dubu talatin da zasu kare butun man kasar, saboda kamar yadda shugaba Obama yace:

Matakin Iran na daura damarar makaman nuclear abu jne dake hadasa barazana ga yankin da kuma duniya baki daya.

Hakan kuwa abin damuwa ne, musman idan aka lura da gaskiyar cewar gwajin da Amerika tayi a karshen mako,na rokokin da zasu kare ta daga hare haren jiragen samany akin Iran basu bai sami nasararda ake bukata ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Yahouza Sadissou