Iran zata mayar da martani game da bukatar Mdd | Labarai | DW | 22.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran zata mayar da martani game da bukatar Mdd

A yau ne ake sa ran Iran zata mayar da martani, a hukumance ga bukatar da Mdd ta gabatar mata, na dakatar da aniyar ta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium.

A dai watan daya gabata ne, Mdd tayi kira ga Iran data daina sarrafa sanadarin na uranium ko kuma ta fuskanci fushin ta.

Idan dai za´ a iya tunawa a jiya ne shugaban addini na Iran, wato Ayatollah Ali Khamenei, ya tabbatar da cewa Iran zata ci gaba da wannan aniya data sa a gaba, don mallakar makamin na Atom.

A ranar 31, ga wannan watan da muke cike ne wa´adin da Mdd ta bawa Iran na dakatar da wannnan aniya ta ta yake karewa.

Matukar kuwa Iran tayi kunnen uwar shegu da wannan al´amari to babu shakka, zata fuskanci fushin Mdd ta hanyar kakaba mata takunkumi.

Har ya zuwa yanzu dai, Iran ta dage kann cewa Nukiliyar da take son kerawa ta inganta harkokin rayuwar mutanen kasar ta ne , amma bata tashin hankali ba.