Iran zata mayar da martani ga Mdd a yau din nan | Labarai | DW | 29.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran zata mayar da martani ga Mdd a yau din nan

A wani lokaci ne a yau din nan ake sa ran shugaban kasar Iran Mahmud Ahmadinajad, zai mayar da martani ga bukatar da kwamitin sulhu na Mdd yayi wa kasar, na dakatar da aniyar ta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium.

A dai ranar alhamis mai zuwa ne, wa´adi n da kwamitin sulhu na Mdd ya debarwa kasar ta Iran yake karewa, wanda bayan sa ne kuma majalisar tace zata dauki mataki.

A dai jiya kafafen yada labaru sun rawaito kakakin gwamnatin kasar ta Iran na yin watsi da barazanar da Amurka tayi wa kasar na kiran asa mata takunkumi, matukar bata aiwatar da umarnin kwamitin sulhun na Mdd.

A wata ganawa da sukayi a birnin Paris, ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus, sun bukaci dangantakar kasa da kasa dasu duba matakan warware rikicin nukiliyar kasar ta Iran ta hanyar ruwan sanyi.

Kasashen na Jamus da Faransa na daga cikin kasashe shidda masu fada aji a duniya da suka yi alkawarin tallafawa kasar ta Iran, ta fannin tattalin arziki da tsaro, matukar tayi watsi da aniyar ta na ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium.