1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran zata gabatar da shawarwari dangane da shirinta na nukiliya

June 10, 2006
https://p.dw.com/p/BuuZ

A takaddamar da ake game da shirin nukiliyar ta Iran ta ce zata gabatar da wasu shawarwari a daura da tayin taimakon da kasashen nan 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu da kuma Jamus suka gabatar mata. Kafofin yada labarun Iran sun rawaito ministan harkokin waje Manushir Mottaki na cewa kasarsa na fatan yin wasu jerin shawarwari na diplomasiya domin samun damar yin nazari ga shawarwarin da kuma canje canjen da gwamnati a birnin Teheran ke son a yi. Ministan harkokin wajen na Iran ya ce kasarsa ta fara nazari akan tayin taimakon da aka gabatar mata. To amma bai fadi lokacin da kasar zata ba da amsa a hukumance ba. Kasashen 5 dai masu ikon hawa kujerar naki a kwamitin sulhu da kuma Jamus sun yi alkawarin bawa Iran taimakon tattalin arziki da fasahohin zamani, idan ta dakatar da shirin ta na nukiliya.