Iran zata ci-gaba da shirin ta na nukiliya, inji shugaba Ahmedinejad | Labarai | DW | 14.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran zata ci-gaba da shirin ta na nukiliya, inji shugaba Ahmedinejad

Shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nijad ya ce ba bu ja da baya a shawarar da ya yanke ta komawa ga aikin bincike a fannin nukiliya duk da gargadin da ake yi cewar ana iya yin karar Iran a gaban kwamitin sulhu na MDD. Shugaba Ahmedi-Nijad ya fadawa manema labarai hakan a wajen wani taron´yan jarida da aka gudanar a daidai lokacin da ake samun hauhawar tsamari dangane da shirin nukiliyar Iran. A ranar alhamis da ta gabata, masu shiga tsakani na kasashen Jamus, Birtaniya da kuma Faransa sun ce duk kokarin da aka yi na shawo kan Iran ta dakatar da shirinta na binciken fasahar nukiliya ya ci-tura. A ranar litinin mai zuwa jami´an kasashen tarayyar Turai da na Amirka da China da kuma Rasha zasu gudanar da shawarwari a birnin London, inda ake sa rai zasu sanya ranar da za´a gudanar da taron gaggawa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa.