Iran zata ci-gaba da bin hanyoyin diplomasiya | Labarai | DW | 05.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran zata ci-gaba da bin hanyoyin diplomasiya

Duk da karar ta da za´a yi a gaban kwamitin sulhu na MDD, Iran ta ce zata ci-gaba da bin hanyoyin diplomasiya don warware takaddamar da ake yi game da shirinta na nukiliya. Kakakin ma´aikatar harkokin waje Hamid Reza Assefi ya fadawa manema labarai cewa kasarsa zata ci-gaba da tattaunawa da Mosko akan shawarar da Rasha ta gabatar don gano bakin zaren warware wannan takaddama. A jiya Iran ta nuna shakku ko za´a koma ga tattaunawa akan shawarar ta Rasha, inda Rasha zata samar da uranium din da Iran din ke bukata. A dai halin da ake ciki gwamnati a Teheran ta ba da sanarwar komawa ga aikin samar da sinadarin uranium gadan gadan kana kuma ba zata yarda a gudanar da bincike na bazata a tashoshinta na nukiliya ba. Shi kuwa shugaban Amirka GWB ya tofa albarkacin bakinshi akan hukuncin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yanke da cewa wani muhimmin sako ne ga gwamnatin Teheran dake nuni da cewa duniya ba zata yarda Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.