1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran tayi ikrarin fara aikin sarrafa uraniyum a tasharta ta biyu

Kasar Iran tayi ikrarin fara aikin sarrafa sinadaren uraniyum a maaikatar sarrafa sinadarenta ta biyu.

Kanfanin dillancin labaru na Iran ISNA ya ruwaito daga bakin wani babban jamiin kasar na fadin cewa a makon daya gabata sun sanya iskar gas a injin sarrafa makamashin kuma an samu nasara da ake bukata.

A dai ranar laraba ne kasar Iran ta tabbatar da cewa,ta kafa sabbin kayan aiki na inganta uraniyum.

Wannan kuwa ya faru ne duk kuwa da barazanar takunkumi da majalisar dinkin duniya takeyi mata game da shirin nata na nukiliya.