1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran tace tana nan kan bakanta

March 10, 2006
https://p.dw.com/p/Bv5N

Kasar Iran tace tana nan akan bakanta na ci gaba da binciken makamashin nukiliya duk kuwa da barazanar takunkumi da take fuskanta.

Ayatollah Ali Khameni,shugaban addini na kasar yace,kasashen yammacin duniya su zasu fi shiga wahala muddin dai sun nemi dakatar da jamhuriyar ta Islama daga samun fasahar nukiliya.

Wannan kalami nasa kuwa ya zo ne bayan hukumar kare yaduwar nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yanke shawarar mika Iran gaban komitin sulhu,wadda take da ikon lakabawa kasar takunkumi.

Sakatare janar Kofi Annan yace akwai yiwuwar ci gaba da shawarwari akan wannan batu,ya kara da cewa har yanzu dai lokaci bai yi ba da zaa lakabawa Iran din takunkumi.

A jiya ne sakatariyar harkokin wajen Amurka Conoleezza Rice tace,kasar Iran itace babbar kalubale dake fuskantar gwamnatin Amurka kuma zata iya zamowa babbar barazana ga tsaron yankin gabas ta tsakiya muddin dai ta mallaki makaman nukiliya.

Ita dai Iran ta sha nanata cewa,shirinta na nukiliya na lumana ne,domin makamashi a cikin gida.