Iran tace ba zata dakatar da inganta uraniyum ba | Labarai | DW | 08.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iran tace ba zata dakatar da inganta uraniyum ba

Maaikatar harkokin wajen Iran a yau ta baiyana cewa kasar iran ba zata dakatar da inganta uranyium ba ta kuma ce barazanar kafa takunkumi na kasa da kasa da akayi mata da cewa,wani makami da ba zayi yi tasi akanta ba.

A ranar jumma ne kasashe 6 da suke kokarin shawo kann Iran ta dakatar da shirin nata suka amince su tattauna batun yiwuwar kafa mata takunkumi.

Kakain maaikatar Muhammad ali hosseini yace dama can kasahen sun saba da wannan barazanar,ya kuma sake jaddadda cewa tattaunawa itace kadai hanya data dace a sasanta wannan rikici.