1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ta yi watsi da wa’adin da aka ba ta .

July 2, 2006
https://p.dw.com/p/Burr

Iran ta yi watsi da wa’adin da ƙasashen yamma suka ba ta na ta ba da masa ga tayin da aka yi mata game da batun warware rikicin makamashin nukiliyanta. Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, ya ce Iran ba za ta ba da amsa ba, sai cikin sabon watanta, wanda zai fara a ran 23 ga wannan watan na Yuli.

Ƙasashe guda 5 masu kujerun dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Jamus, sun yi wa Iran tayin ba ta damar cin moriyar wasu fa’idoji, idan ta amince ta tsai da sarrafa sinadarin Yureniyum da take yi. Su dai ƙasashen Yamman na fargabar cewa, Jumhuriyar Islaman ta Iran, za ta ƙera makaman nukiliya ne, idan aka ƙyale ta ta ci gaba da inganta fasahar wannan makamashin. A daura da haka, Iran ɗin ta sha nanata cewa, burinta ne ta samar wa kanta tabbattacen tushe na samad da makamashin wutar lantarki.